Wasu masu damfara ta kafar yanar gizo sun hallaka wani jami’in hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC tare da jikkata abokin aikinsa a Jihar Anambra.

Lamarin ya faru ne a jiya Juma’a a lokcin da jami’an hukumar suka kai sumame maboyar batagarin a Jihar.
Bayan zuwan jami’an ‘yan damfarar suka bude musu wuta da harbe-harbe wanda hakan ya tilastawa jami’an tserewa.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne dai bayan da jami’an suka yi yunkurin kama mutanen da ake zargi na cikin wata kungiya ta damfarar yana gizo.

Jami’in da mutanen suka kashe na da muƙamin Mataimakin Sufurtanda a hukumar, inda kuma wanda aka jikkata ke kwance a Asibitin ana kula da lafiyarsa.

Baban Ofishin hukumar ta EFCC da ke Jihar Enugu ne ya tura jami’an jihar ta Anambra don gudanar da aiki.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ta Anambra Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce su na ci gaba da gudanar da bincike, inda kuma suka kama wanda ake zargi da kisan, tare da kwace bindigar, inda ya ce zai yi karin bayani nan gaba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: