Kungiyar tuntuba ta Arewa Consultative Forum ta ce tsadar man fetur da ake fuskanta ce ta sa mutane su ka je domin diba yayin da mota ta fadi a jihar Neja.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ta na mai jajantawa dangane da rasa rayuka sama da 80 da aka samu.

Sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Tukus Muhammad Baba sakataren yada labaran kungiyar, sun nuna damuwa a kan halin da al’umma ke ciki.

A cewar sanarwar, duk da cewar dabi’a ce da ake samu bayan faduwar tankar mai, sai dai lamarin ya fi kazanta a yanzu saboda karancin wayar da kai da kuma halin da mutane su ka tsinci kansu a ciki.

Sannan sun bukaci da a dauki matakai da za su hana faruwar haka a nan gaba.

Motar man ta fadi ne a Dikko Junction a karamar hukumar Gurara da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: