Gwamnatin Najeriya ta sake bayar da kwangilar aikin titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria har Kano.

Ministan ayyuka a ƙasar David Umahi ne ya bayyana wanda ya ce za a kammala aikin kaso na biyu daga Abuja zuwa Kaduna.

An bai waa kamfanin Infoquest Nigeria Limited kwangilar kammala aikin.
Idan za a iya tunawa, a makon jiya ministan ya tabbatar da cewar daga yanzu aikin ba zai sake tsayawa ba.

Har ma ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya ce za a kammala aikin nan da watanni 14 masu zuwa.
Aikin dai ya shafe fiye da shekara shida ana yinsa kuma har yanzu ba a kammala ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: