kalla mutane uku ne su ka mutu sakamakon hatarin wani kwalekwale da ya auku a jihar Rivers.

An dakko mutanen ne daga Fatakwal zuwa Bonny Island.
Lamarin ya faru a yammacin Lahadi a yankin Yellow Plaatform da ke dab da Bonny.

Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata, mai magana da yawun yan sanda a jihar Grace Iringe Koko ta ce an ceto mutane 19 yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane uku

Jami’ar ta ce su na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin domin gano sanadin faruwar haka.
Shugaban kungiyar ma’aikatan jiragen ruwa ta Najeriya reshen jihar Rivers ya ce iska mai karfi ce ta haddasa hatsarin.