‘Yan sanda a Jihar Ondo sun gurfanar da wani matashi a gaban Kotu sakamakon hallaka mahaifinsa da yayi.
Matashi mai shekaru 32 ya hallaka mahaifinsa nasa ne mai shekaru 68, sakamakon mahaifin nasa yaki saya masa sabon babur.

A yayin gabatar da wanda ake zargi a gaban Alkali a jiya Juma’ a dan sanda mai gabatar da ƙara Abdulateef Suleiman, ya shaidawa kotun cewa matashin ya kashe mahaifinsa ne a yankin Isua Akoko da ke cikin Ƙaramar Hukumar Akoko ta Jihar.
Mai gabatar da karar ya ce jami’an ’yan sanda sun gano cewa bayan mahaifin ya gaza sayawa matashin babur din ne, hakan ya haifar da rashin jituwa tsakanimsu, inda ya shake mahaifin nasa har takai ga ya rasa ransa.

Sai dai bayan gabatar da shi a gaban Kotun Alkaliyar Kotun Funke Akinboboye ta bayar da umarnin tsare matashin a gidan gyaran hali na Jihar, zuwa lokacin da za ta ji daga ofishin Daraktan Gurfanarwa na Gwamnati.

Sannan Alkaliyar ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Fabrarun 2025.