Rundunar yan sanda a Kano ta kama shugaban hukumar karbar korafe-korafen al’umma da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano wato Muhuyi Magaji Rimingado, rundunar ta damke shugaban hukumar ne a jiya Juma’a.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kama Muhuyin ya biyo bayan wani sumamen yan sanda wanda mataimakin sufartandan yan sanda Ahmed Bello ya jagoranta, wanda ya tabbatar da cewa umarni aka bashi ya damke shugaban hukumar.

Wata majiya ta bayyana cewa, kama Muhuyin yana da alaka da wani bincike wanda ke da alaka da shugaban kamfanin samar da kayan aikin noma Bala Muhammad Inuwa, wanda ake zargi da karkatar da kudi kimanin Naira biliyan 4.

An fara shari’ar kan binciken a watan Nuwanban shekarar 2023 a babbar kotun wacce mai shari’ah Hafsat Yahaya ta jagoranta, inda ta yi umarnin karbe wasu kadarori da ake zargin su na da alaka da binciken.

Sai dai a watan Disambar shekarar 2023 ne, Bala Muhammad Inuwa ya shigar da sabuwar kara a gaban mai shari’ah Aisha Ya’u ta wata babbar kotun jihar Kano, bisa bukatar kotun ta bayar da umarni janye jami’an yan sanda a kofar wani kamfani da aka ajiye kayan da aka kwace.

Sai dai bayan kamashi ‘yan sandan sun bayar da belinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: