Asusun tallafawa yara da mata na majalissar dinkin duniya UNICEF ya jaddada kokarinsa na goyon baya, don rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihohin Jigawa, Kano da kuma Katsina.

Shugabar UNICEF jihar Kano Rahama Mohammed Farah ce ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai, a wajen taron ranar ilimi ta duniya jiya Juma’a a jihar Kano.

Ya kuma bayyana kudirinsu na habbaka bangaren na ilimi, inda ya ce jihohin Arewa maso Yamma su ne na biyu a yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.

Inda ya kara da cewa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihohin na Kano, Jigawa da Katsina ya yi yawa, inda rashin hanyoyin koyo masu inganci ya ke kara ta’azzara ga yaran da ba su samu sukun zuwa makaranta ba.

Ya kuma bayyana cewa akwai yara miliyan 10.2 da ba sa zuwa makarantar, wadanda kashi 16 cikin 100 daga jihohin Kano, Jigawa da Katsina su ke bisa wata kididdigar da hukumar MICS ta fitar a shekarar 2021.

Muhammad ya ce bangarorin da za su bayar da muhimmanci wajen habakawa sun hadar da kyautata walwalar malaman makaranta, tsaftar jikin yaran, muhallansu da kayan koyo da koyarwa, sai kuma ruwan sha da yanayin koyon da ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: