Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta musanta labarin cewa rundunar ta kama, shugaban hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundutar ta Kasa Olumuyiwa Adejobi ya fitar a yau Laraba, ya ce rundunar ba kama Muhyi tayi ba,gayyatar shi tayi bisa wasu zargi da ake yi masa.
Sanarwar ta ce a ranar juma’a 17 ga watan janairun 2025 ,babban sufeto ‘yan sanda na kasa ya karbi kara kan ana zargin Muhuyi Magaji, bisa wasu dalilai dan haka hukumar ta gayyace shi domin tayi bincike kan lamarin.
Rundunar ta ce tana sanya ran Muhuyi zai bata hadin kai wajen gudanar da bincike da take yi akansa.

Sannan rundunar ta yi gargadi kan cewa dukkan wani rahoto na cewa ta kama Muhyi ba gaskiya bane, inda ta yi kira ga kafafan yada labarai da al’umma da su gujewa yada maganar da ba ta da tushe balle makama.

A karahe rundunar ta ce a shirye take wajen bin doka da oda da kuma bin ka’ida wajen gudanar da ayyukanta.