Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce an hallaka jamianta 22 yayin da su kuwa su ka hallaka yan ta’adda sama da 70 a arewa maso gabashin Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun helkwatar Edward Buba ya fitar, ya ce daga cikin jami’an tsaron da aka hallaka har da na sa kai da ake hadin gwiwa da su.
Buba ya ce daga cikin wadanda aka hallaka har da kwamandojin mayakan Boko Haram.
Daga ciki kawai Malam Umar, Abu Yazeed da wani mai suna Talha.

A cewarsa, an samu nasarar nentsakanin ranakun 16 zuwa 25.

Ko da cewar jami’an sojin sun dakile harin da mayakan su ka kia musu a wani sansaninsu, sai dai an kashe wasu sojoji tare da jikkata wasu da dama.