Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana aniyarta na ciyar da mabukata 189,000 a watan azumin Ramadana na shekarar ta 2025 da ke tafe.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Safir Musa ne ya tabbatar da hakan a yayin ganawa da manema labarai a jiya Litinin bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar.

Kwamishinan ya ce gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya amince da shirin, tare da bayar da umarnin fitar da Naira biliyan 4.8 domin ciyar da mabukata a fadin Jihar.

Acewar Kwamishinan shirin ciyar da mabukatan zai taimaka matuka, wajen taimakon mabukatan a watan na Azumin.

Kazalika Sagir Musa ya bayyana cewa gwamnatin Jihar, hadin gwiwa da kananan hukumomin Jihar ne za su samar da kudaden da za a gudanar da shirin ciyarwar, inda gwamnatin Jihar za ta samar da kashi 55 cikin 100 na kudin, yayin da kananan hukumomin kuma za su samar da kashi 45 cikin 100 na kudin.

 

Bugu da kari ya ce an kuma kara yawan cibiyoyin da suke dabawa tare da raba amincin daga 609 na shekarar 2024 da ta gabata zuwa 630 a shekarar nan 2025.

Har ila yau ya kara da cewa dukkanin cibiyon da aka bude za su dunga bai’wa kowanne mutum kalar abinci uku a kowacce rana.

Sannan Kwamishinan ya ce Majalisar Jihar ta amince da yin kunu, kosai da kuma shinkafa dafa-duka, yayin da kowacce cibiya za ta ciyar da mutane 300.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: