Gwamnatin jihar Kano ta janye karar da ta shigar kan masu zanga-zanga tsadar rayuwa a jihar.

Babban lauyan gwamnaatin Kano kuma kwamishinan Shari’a Barista Haruna Isah Dederi ne ya janye karar a jiya Litinin.

Wata ƴar kungiyar fararen hula Rachael Adio ne ya bayyana haka a yau Talaata.

Ta ce tun a ranar 5 ga watan Nuwamba su ka hukaci Kwamishinan shari’a n ajihar d aya yi mafani daa sashe na 211(1) cikin baka da (c) cikin baka n akundin tsarin mulkin kasa da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 1999.

Yan kungiyar fararen hular ta bukaci a yi watsi da karar da kaa shigar da waɗanda aka kama a yayin zanga-zanga da aka yi a ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agustan shekarar da ta gabata.

Sannan ta yabawa kwamishinan shari’a bisa janye karar da ya yi a kan wadanda aka kama.

Haka kuma ta ce za su ci gaba da kasancewa masu fafutular tabbatar da adalci don kare fararen hula a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: