Babban Kotun Jihar Kano ta haramtawa rundunar ’yan sanda sake kamawa, tsarewa ko kuma gayyatar Shugaban Hukumar karbar korafe-korafen jama’a da hana cin hanci da rashawa na Kano Muhyi Magaji Rimin gado.

Kotun ta bayar da umarnin ne bayan karar da Babban Lauyan jihar da hukumar, tare da Rimin Gado suka shigar gabanta.
Wadanda ake kara sun hada da rundunar ’yan sanda ta Kasa, Sufeto-Janar na ’yan sanda da Mataimakinsa mai kula da Shiyya ta Daya da Kwamishinan ’Yan Sandan Kano da ASP Ahmed M. Bello da kuma Bala Muhammad Inuwa.

Sannan Kotun ta kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu mai kamawa.
