Wata tankar man fetur ta sake fashewa a garin Kusogbogi da ke tsakanin Ƙananan Hukumomin Agaie da Lapai ta Jihar Neja.

Rhotannin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a jiya Litinin da misalin karfe 6:oo na yamma.
Bayan fashewar tankar man ba a samu a sarar rasa rayukan mutane ba.
Wani mazaunin garin Lapai mai suna Malam Mahmud Abubakar ya bayyana cewa tamkar ta yi hadarin ne sakamakon gudun wuce sa’a da direban motar ke yi, inda ya daki wata babbar motar dakon kaya da ke tsaye, inda ta kama da wuta.

Lamarin dai ya faru ne kasa da mako guda da wata tamkar mai ta fadi a Dikko Junction da ke hakamar hukumar Gurara ta Jihar Neja, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 98.
