Majalisar zartarwar gwamnatin tarayya ta amince da ƙarasa aikin gina wasu tituna guda huɗu, bayan binciken ƙwaƙƙwafi akan su waɗanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari.

Ministan ayyuka David Umahi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai jiya Litinin, bayan zaman majalisar karo na uku a wannan shekarar.
Ya ce an fara amincewa ne da mayar da titin Odupani-Itu-Idedem Item da ke Ekpene a jihohin Cross River da Akwa Ibom zuwa mai hannu biyu, akan kuɗi Naira miliyan dubu 55 ga kamfanin Decon Construction Nigeria Limited.

Sai kuma titin Ibadan zuwa Ilorin ɓangaren na biyu da ke Ogbomosho a jiyar Oyo, akan kuɗi Naira miliyan dubu 147 ga kamfanin GRVe.

Na uku shi ne ƙarasa aikin titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano ɓangare na biyu mai tsawon kilomita 164, akan kuɗi Naira miliyan dubu 507.
Na ƙarshe shi ne aikin ginin gadar sama a Abapka da ke Enugu domin rage cinkoso, akan kuɗi Naira miliyan dubu 24 ga kamfanin CCECC.
A ƙarshe ministan ya bayyana cewa kamfanin Info West Nigeria Limited da su ke aikin titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano ɓangaren farko, su ne dai aka sake bai’wa ci gaba da aikin ɓangaren na biyu.