The new logo of the privatised Nigeria oil company is seen at the NNPC Mega Gas Station in Abuja, Nigeria August 30, 2022. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Kamfanin Mai na ƙasa NNPCL ya rage farashin siyar da mai, a ɗaukacin gidajen siyar da mai mallakinsa da ke faɗin ƙasar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, jami’inta ya nazarci cewa gidajen mai mallakin kamfanin na NNPCL da yammacin jiya Litinin a birnin tarayya Abuja, su na siyar da kowacce litar man akan farashin Naira 880 a maimakon Naira 965 da ake siyarwa a baya.

Ragin farashin man na kamfanin NNPCL ɗin na zuwa ne dai, kwanaki kaɗan bayan kamfanin mai na Dangote sun sanar da rage nasu farashin.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai matatar mai ta Dangote ta tabbatar da rage farashin man ga masu dakonsa, daga Naira 890 zuwa Naira 825 akan kowace lita, tare da bayyana cewa sun yi Ragin ne don sauƙaƙawa ƴan Najeriya sakamakon zuwan watan Azumin Ramadan.

Masu aikin siyar da man a gidajen man na NNPCL daban-daban da ke birnin tarayya Abuja, sun tabbatarwa da ƴan Jarida cewa labarin na rage farashin man gaskiya ne.

Haka zalika daga jihar Legas ma an tabbatar da samun ragi akan farashin man, inda kowacce lita ɗaya ake siyarwa da ita akan Naira 860 a dukkan gidajen man mallakin kamfanin na NNPCL.

A nasa ɓangaren mai magana da yawun kamfanin NNPCL Olufemi Soneye ya bayyana cewa, tun biyo bayan sauya fasalin kamfanin man, su kan saisaita farashinsa lokaci zuwa lokaci gwargwadon yadda kasuwa ta kasance.Kamfanin Mai na ƙasa NNPCL ya rage farashin siyar da mai, a ɗaukacin gidajen siyar da mai mallakinsa da ke faɗin ƙasar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, jami’inta ya nazarci cewa gidajen mai mallakin kamfanin na NNPCL da yammacin jiya Litinin a birnin tarayya Abuja, su na siyar da kowacce litar man akan farashin Naira 880 a maimakon Naira 965 da ake siyarwa a baya.

Ragin farashin man na kamfanin NNPCL ɗin na zuwa ne dai, kwanaki kaɗan bayan kamfanin mai na Dangote sun sanar da rage nasu farashin.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai matatar mai ta Dangote ta tabbatar da rage farashin man ga masu dakonsa, daga Naira 890 zuwa Naira 825 akan kowace lita, tare da bayyana cewa sun yi Ragin ne don sauƙaƙawa ƴan Najeriya sakamakon zuwan watan Azumin Ramadan.

Masu aikin siyar da man a gidajen man na NNPCL daban-daban da ke birnin tarayya Abuja, sun tabbatarwa da ƴan Jarida cewa labarin na rage farashin man gaskiya ne.

Haka zalika daga jihar Legas ma an tabbatar da samun ragi akan farashin man, inda kowacce lita ɗaya ake siyarwa da ita akan Naira 860 a dukkan gidajen man mallakin kamfanin na NNPCL.

A nasa ɓangaren mai magana da yawun kamfanin NNPCL Olufemi Soneye ya bayyana cewa, tun biyo bayan sauya fasalin kamfanin man, su kan saisaita farashinsa lokaci zuwa lokaci gwargwadon yadda kasuwa ta kasance.

Leave a Reply

%d bloggers like this: