Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 26 sakamakon barkewar cutar sankarau a wasu kananan hukumomi hudu na Jihar.

Kwamaishinan lafiya na Jihar Dr Yunusa Isma’il ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Jihar.

Kwamishinan ya ce baya ga mutanen da suka mutu, an samu mutane 248 da ake kyautata zaton sun kamu da cutar.

Isma’il ya ce daga cikin mutane 11 da aka gwada a ɗakin gwaje-gwaje an gano cewa uku daga cikinsu na cikin qoshin lafiya.

Kwamishinan ya bayyana cewa ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Gwandu, Aleiro, Jega da kuma Argungun.

Ya ce a Gwandu mutane 15 ne suka rasa rayukansu, yayin da a Jega mutane shida suka mutu, sai Argungun mai daya, da kuma hudu a Aleiro.

Har ila yau kwamishinan ya ce a halin yanzu an bude sansanonin da aka killace mutanen da suka kamu, inda gwamnatin jihar ta fara ɗaukar matakan daƙile cutar ciki har da neman alluran rigakafin, inda ya bukaci mutane da su gaggauta zuwa asibiti mafi kusa domin yin gwaji a duk lokacin da su ke cikin halin rashin lafiya don tabbatar da lafiyarsu.

Kazalika ya bukaci mutane da su kauracewa zuwa sansanonin mutanen da aka kebe masu dauke da cutar, tare da wanke ‘ya’yan itauwa kafin ci, don gujewa kamuwa da cutar
Kwamnashinan ya ce gwamnan Jihar Nasir Idris ya bayar da tallafin naira miliyan 30 domin siyan magunguna da sauran kayayyaki domin ɗaukar matakan daƙile cutar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: