Gwamnatin Jihar Sokoto ta gargadi mazauna Jihar da su kula matuka sakamakon barazanar barkewar cututtuka masu yaduwa a wasu Kananan hukumomin Jihar.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Dr Faruk Umar Wurno ne ya tabbatar da hakan ta cikin wani jawabi da ya fitar a yau Talata.
Kwamishinan ya bukaci al’ummar Jihar da su zama cikin shirin dakile cutar ta Sankarau da alamominta suka fara bayyana a Jihar.

Wurno ya bayyana cewa ya zama dole dukkan wasu alamomi da aka gani a dauka tare da shiga da su dakin gwaji, don bincikawa do tabbatar da lafiyar mutum.

Acewarsa ma’aikatarsa za ta sanya idanu akan jami’an lafiya na gwamnati da masu zaman kansu don ganin an dakile yaduwar cutar a fadin Jihar.

Kwamishinan ya ja kunnen al’ummar Jihar da cewa su kasance a kowamne lokaci masu kula don daukar matakin kariya na gujewa daukar cutuka masu yaduwa.

Sannan yayi kira mazauna Jihar da su dunga gaggawar sanar da jami’an lafiya mafi kusa da su, daga lokacin da suka ga wata alama ta rashin lafiya, irin ta zazzaɓi ko ciwon kai mai tsanani da dai sauransu.

Kwamishinan ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da tsaftar jiki da na muhalli, tare da bukatar mutane da su yi iya bakin koƙari wajen kauracewa shiga cikin cunkoso tare da zama a gurin da iska ta ke.

A karshe yayi kira ga mutane da su kai rahoton dukkan wata alama da aka gani ta cutar ko ta wata rashin lafiya da ba a saba gani ba ga jami’an lafiya mafi kusa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: