Tsofaffin Ma’aikata a Jihar Kaduna, sun gudanar da zanga-zanga, tare da bai’wa gwamnan Jihar Uba Sani wa’adin mako biyu da ya biya su hakkokinsu.

Tsofaffin ma’aikatan Jihar ta Kaduna sun gudanar da zanga-zangar ne a yau Talata, inda suka bayyana aniyarsu ta tarewa a gidan gwamnatin har zuwa lokacin da za a biya musu hakkokinsu.

Jagoran masu zanga-zangar Farfesa Nate Danjuma da ya jagorance su zuwa Sir Kashim Ibrahim House, ya ce mambobinsu na mutuwa saboda yunwa, da halin rashin lafiya bisa rashin kulawa da ba sa samu.

Acewarsa a kowacce rana su na rasa mambobinsu saboda halin yunwa, da kuma kudin da za su Asibiti, tare da rasa muhallansu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: