Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ya fara neman wani Jami’inta ruwa a jallo, sakamakon hallaka wani mutum da ke bacci ta hanyar bude masa wuta da yayi bayan shan kayan maye.

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin unguwar Angwan-Kaje da ke yankin Maitumbi karamar hukumar Chanchaga a Minna ta Jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da fatuwar lamarin ga manema labarai a yau Talata, inda ya ce jami’in yayi aika-aikar ne da misalin karfe 3:00 na dare.

Kakakin ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar Shuwala Danmamman, ya umarci Baturen ‘yan sandan yankin na Maitumbi da ya tabbatar da ganin an kamo jami’in domin gudanar da bincike akansa.

Abiodun ya ce kwamishinan ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da hukunta jami’in, bayan kammala bincike, inda kuma za a sanar da mutane matakin da aka dauka kansa.
Sai dai Wasu Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’in da ake zargi, na aiki ne da ofishin ‘yan sanda na Maitumbi, inda ya yi aika-aikar bayan buguwa da yayi bayan shan kayan maye.
Majiyar ta ce bayan shan kayan maye jami’in ya dauki bindigasa, tare da yin harbin kan mai uwa da wabi ga mutanen da ke kusa dashi.