Gwamnatin tarayya ta musanta rade-raden da ke yawo cewa ana kashe kiristoci ba tare da wani dalili ba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatr harkokin Wajen Najeriya ta fitar a yau Juma’a, ta ce masu yada irin wadannan rahotanni su na yi ne da nufin sauya tunanin Kasashen ketare akan Najeriya, musamman Kasar Amurka don ta bayyana Najeriya a matsayin Kasar da ake da kokonto akanta.

Sanarwat ta kara da cewa matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Jihohin arewacin Kasar, inda mafiya yawa Musulmi ke cikinta, hakan ba yana nufin kai wa wasu mabiya wani addinin hari ba ne.

Ma’aiakar ta bukaci da mutane da su yi watsi da rade-raden da babu gaskiya a cikinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: