Hukumar yaki a masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC ta kama, tare da gurfanar da wata mata da mijinta da ake zargi da amfani da sunan uwar gidan gawamnan Jihar Katsina Malam Umar Dikko Radda, wato Hajiya Fatima Dikko Radda wajen yin damfara naira miliyan 197.75.

EFCC ta gurfanar da mutanen ne a gaban babbar kotun Jihar Kaduna karkashin jagorancin mai shari’a Amina Bello, tare da wasu mutane biyu da ake zargi da taimaka musu wajen aikata damfarar.

Matar mai suna Hafsat Kabir Lawal da mijinta mai suna Baba Sule Abubakar Sadiq, sai sauran mutanen biyu sun hada Abdullahi Bala da Ladani Akindele.

Bayan gurfanar da su a gaban kotun a jiya Alhamis EFCC ta bayyana cewa mutanen sun hada kai ne wajen amfani da sunan Hajiya Fatima Radda wajen samun canjin dala daga wani mai yin sana’ar canji, inda matar ta gabatar da kanta a matsayin Fatima Radda, tare da bukatar neman a yi mata canjin dala.

Ya yinda kuma Mijin matar ya sayi layuka, tare da yi musu rajista da sunan Fatima Dikko Radda, don kawar da hankalin mai amfani da manhajar True Caller.

EFCC ta kuma ce Matar ta nemi da a yi mata canjin, inda suka turawa da mai canjin lambar asusun bankin da zai tura kudin kafin ta aike masa da dalar, inda ta karbi Naira miliyan 89 daga hannun wani mutum mai suna Aminu Usman kuma aka biya kudin ta bankin Taj bank mai dauke da sunan Abdullahi Bala da nufin za ta tura masa dala 53,300, sannan matar ta sake karbar Naira miliyan 108, da zummar tura masa dala 118,000.

Laifi dai da ya sabawa Sashe na 1(1) na dokar Zamba da kuma sauran manyan Laifuka na Shekarar 2006.

Sai dai dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta zargin da ake yi musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: