Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta dakatar da hukuncin da ta yi na ranar 10 ga watan Janairu 2025 kan rikin da ke faruwa a Masarautar Kano har zuwa lokacin da kotun Kolin Kasar za ta yanke hukuncin Karshe akan rikicin.

Kotun da dakatar da hukuncin ne a zamanta na yau Juma’a, karkashin kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Justice Okon Abang, a karar da Aminu Babba Dan agundi ya shigar.

Hukuncin da kotun ta yanke ya amince da dakatar da dokar shekarar 2019 da ta kafa sabbin masarautu biyar, inda kotun ta dakatar da hukuncin har zuwa lokacin da kotun ta koli za ta yanke hukunci.

Sai dai a hukunci na farko da kotun ta yanke ta bayyana cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sanya baki a cikin rikicin masarautar, inda ta ce Babbar kotun Jihar ta Kano ce kadai ta ke da hurumin yanke hukunci kan dukka wani rikici da ya shafi sarautara ta Kano.

A zaman kotun na yau Mai shari’a Abang ya ce akwai matakin daukaka kara a gaban kotun koli, kuma dole ne a kare batun da ake shari’a a kansa.

Kotun ta kuma hana gwamnati aiwatar da hukuncin na ranar 10 ga watan na Janairun wanda ya soke rushen sabbin masarautun da kuma dawo da Sarki Sanusi II, sannan kotun ta bayar da umarnin cewa a ci gaba da zama akan matsayin da ake akai har zuwa lokacin da kotun koli ta yi hukunci karshe akai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: