Kungiyar matasan jam’iyyar SDP sun yi fatali da sauya shekar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufa’i ya yi zuwa jam’iyyar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da shugabanta Kwamred Abdulsamad Bello ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta bayyana cewa kungiyar ta matasan SDP ba su amince da komawar Elrufa’i cikin jam’iyyar ba, inda kungiyar ta bayyana zargin cewa ya koma jam’iyyar ne da nufin mamaye ta domin biyan bukatar a siyasa.

Bugu da kari ya bayyana cewa Elrufa’i ya shiga SDP ne bayan ya inganta ta ba sai don ya rushe jam’iyyar kafin ta samu damar dagawa, da kuma haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin ‘ya’yan Jam’iyyar.

Acewar Kwamred Bello ko kadan Nasir Elrufa’i bai cancanci shiga cikin jam’iyyar ba ta fuskar ɗabi’a da kuma siyasa, inda kungiyar ta soki shugabancin jam’iyyar ta SDP kan abin da ta kira da yarjejeniya ta boye, wadda ta bai’wa Elrufai damar shiga cikin jam’iyyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: