Jam’iyyar SDP a Najeriya ta bayyana ta zargi jam’iyyar APC da yunkurin yin barazana ga wadanda ke sauya sheka zuwa wata jam’iyyar.

Mai magana da yawun SDP Rufus Aiyenigba ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Juma’a.

Kakakin ya ce Jam’iyyar APC na amfani da jami’an tsaro wajen yiwa ‘yan adawa barazana, kan sauya shekar da suke yi zuwa jam’iyyarsu ta SDP.

Rufus ya bayyana cewa sun samu rahotan cewa ana yunkurin dakile sanannun ‘yan siyasa da ke shirin ficewa daga APC don haifar da tsoro a harkokin siyasa, wanda hakan ke nuna cewa ana dakile su bisa shirinsu na komawa jam’iyyar ta SDP.

Kazalika ya kara da cewa na Jam’iyyar SDP na da tabbatattun bayanai kan yadda jam’iyyar APC ta damu matuka da yadda SDP ke kara karfafa, wanda hakan ya sanya APC ta dauki matakin lalubu zarge-zargen da babu gaskiya a cikinsu akan mambobin SDP.

Acewarsa Jam’iyyar APC ta shirin fara tuhumar tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai bayan ficewar da yayi daga jam’iyyar ta APC zuwa SDP, tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Sannan ya kuma ce sun samu labarin cewa gwamnatin tarayya ta bayar da umarni ga hukumominta da su haramtawa Nasir El-Rufai barin Najeriya, inda ya sake zargin gwamnatin jihar Kaduna da bin sahun gwamnatin tarayya wajen yin barazana ga ƴan adawa.

Ya ce APC ta na yin hakan ne da nufin murkushe jam’iyyar SDP tare da yin barazana ga dimokuradiyyar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: