Dan takarar gwamnan a Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023 a jihar Legas Dr Abdul-Azeez Adediran, wanda ake kira da Jandor ya sauya sheka daga jam’iyyasa ta PDP zuwa Jam’iyyar APC.

Adediran ya bayyana ficewarsa daga PDP ne a yau Litinin, makonni kadan bayan sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ta sa ta PDP.
Acewarsa ya fice daga PDP ne sakamakon rashin ladabtarwa da kuma ricikin cikin gida da jam’iyyar ke fama dashi, inda ya ce wannan shi ne babban dalilin da ya sanya ya fice daga jam’iyyar.

Kazalika ya ce kafin barin nasa PDP sai da ya tattauna da abokansa na siyasa da magoya bayansa, tare kuma da shugabannin wasu jam’iyyu da suka hada da ADC, YPP, da SDP, daga bisa kuma ya yanke shawarar komawa jam’iyyar ta APC.

Jandor ya shaidawa magoya bayansa cewa komawarsa jam’iyyar APC, hakan zai taimaka matuka wajen ci gaban Jihar, inda ya bukaci da suma su shigo jam’iyyar don kara samun ci gabanta.
Dan takarar ya nuna takaicinsa kan yadda jam’iyyar ta gaza magance matsalar cin dunduniyar ta tun a lokacin zaben na 2023.