Gwamnatin jihar Kano karkashin jagoranci gwamna Abba Kabir Yusuf ta umarci dukka ma’aikatan gwamnatin Jihar da su tantance albashinsu na watan nan na Maris kafin a biya su don hana samun kura-kurai a ciki.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ibrahim Faruk ne ya tabbatar da haka a yau Litinin a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Jihar.

Sakatare ya bayyana cewa gwamnantin ta dauki wannan matakin ne bayan yin korafi akan yadda aka zabtare albashi daga Ma’aikatan na Watan Janairu da ya gabata.

Faruk ya ce za a yi tantancewar ne ta hanyar kafe bayanin albashin Ma’aikatan a ma’aikatun gwamnatin Jihar da hedkwatar kananan hukumomi 44 na fadin jihar don a yi tantancewar cikin sauki.

Alhaji Faruk ya ce kowanne ma’aikaci zai duba bayanin albashinsa da aka kafe domin tabbatar da sunayensu da kuma adadin albashin da za a ba su.

Sakatare ya kara da cewa dukkan wani ma’aikaci da ya ga an zabtare masa albashinsa zai iya shigar da korafi ga Ma’aikatar da ya ke aiki ko kuma hukuma don yi masa gyara.

Har ila yau ya ce gwamnatin ta kuma kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban Ma’aikatan Jihar Alhaji Abdullahi Musa, inda kuma kwamitin zai gudanar da aikin tantancewar cikin gaggawa don ganin an biya ma’aikatan albashinsu na watan na Maris akan lokaci.

Acewarsa tantancewar ba za ta shafi ayyukan ma’aikatun gwamnati da hukumomin Jihar ba, inda ya bukaci da ma’aiktan da su dauki tantancewar da muhimmanci don kaucewa dukkan wata matsala akai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: