Kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen Jihar Kaduna CAN ta yabawa gwamnan Jihar Kaduna Malam Uba Sani bisa yadda yake tafiyar da salon mulkin Jihar.

Shugaban kungiyar na Jihar Rabran Calen Ma’aji ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi a gurin buda baki da gwamnan ya shiryawa Limaman mabiya addinin kirista da manyan shugabannin Kiristoci a gidan Sir Kashim Ibrahim Jihar.
Ma’aji ya ce kungiyarsu ta kiristoci ba za ta gushe ba wajen yiwa gwamnan Uba Sani addu’ar samun nasara, duba da yadda yake sanya su a cikin harkokinsa.

Shugaban ya bayyana cewa gwamnan Uba Sani ya kasnce mai hada kan kowanne bangare, kuma hakan na bai’wa bangarorin damar gudanar da dukkan abinda ya kamata na ci gaban Jihar ta Kaduna.

Ma’aji ya kuma kara da cewa yadda gwamnan Uba Sani ke tafiyar da mulkin Jihar, hakan ya nuna cewa gwamnatinsa ta yi zarra da gwamnatin baya da ta shude, wanda hakan ya bai’wa mabiya addinin kirista na Jihar kwarin gwiwar jin sun zamo ‘yan Jihar.
Bugu da kari ya ce a shekarar 2023 da ta gabata gwamna Uba Sani ya halarci taron bikin kiristoci na Jihar wanda ya kasance karon farko, inda kuma ya yi musu alkawarin cewa zai ci gaba da halarta kowacce shekara.
Acewarsa don haka ba za su gaza ba wajen yiwa Uba Sani addu’o’in domin ganin ya ci gaba da guanar da ayyukan alkhairi a koda yaushe.