Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa dakatarwar da shugaban Kasa Bola Tinubu ya yiwa gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa da kuma Majalisar dokokin Jihar hakan ka iya bata sunan Najeriya.

Goodluck ya bayyana hakan ne a yau Asabar a lokacin da ya ke jawabi a matsayin shugaban taron gidauniyar Haske Satumari da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana takaicinsa kan yadda shugaba Tinubu ya dauki matakin dakatar da Fubara, yana mai cewa hakan ba kimar tsofaffin shugabanni ba ce sanya baki a harkokin siyasa don ka da a ƙara damalmala lamarin.

Goodluck ya kara da cewa ya kama a kula sosai wajen martaba Kasa da kuma yawan hannun jarin da ke shigowa wanda ke da nasaba da matakan bangaren zartarwa, majalisar dokoki dama ɓangaren shari’a ke dauka.

Jonathan ya kuma yi Allah-wadai da yadda wani mutum daya ke bai’wa bangaren shari’a umarni kan abin da za su yi, inda ya ce hakan na ragewa al’umma kwarin gwiwar samun adalci daga bangaren shari’a.
Acewarsa matakin da bangarorin zartarwa da Majalisar dokoki suka dauka na dakatar da Fubara hakan batawa Najeriya suna ne.