Ƙungiyar shugabannin Kananan hukumomin Najeriya ALGON ta bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fara turawa Kananan hukumomin Kasar kudaden su ba ne Kai tsaye sakamakon wasu matakan da har yanzu ba a kammala su ba.

Shugaban kwamitin amintattun na kungiyar Odunayo Alegbere ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a birnin tarayya Abuja bayan kammala zaman tattaunawa da kungiyar ta yi.

Alegbere ya ce an bai’wa Kananan hukumomin Kasar umarnin bude asusu a jiyar banki na babban bankin Kasa na (CBN) domin ganin an saukaka aiwatar da tsarin tura musu kudaɗen kai tsaye.

Shugaban ya jinjinawa gwamnatin tarayya bisa ci gaban da aka samu, duk da cewar har yanzu ba a kammala tsarin ba, inda ya ce hukuncin Kotun Koli kan ‘ƴancin cin gashin kan Kananan hukumomin Kasar babbar nasara mai girma.

Alegbere ya kara da cewa gwamnatin ta tarayya na ƙoƙarin ganin aiwatar da hukuncin kotun ta koli, da ya shafi ƴancin gudanarwa da ƴancin sarrafa kuɗaɗe ga ƙananan hukumomin.

Bugu da kari ya ce bayar da kuɗaɗe kai tsaye ga ƙananan hukumomin hakan zai taimaka matuka wajen rage talauci a Kasar, wanda hakan zai bai’wa ƙananan hukumomi damar amfani da kuɗaɗensu da kuma gudanar da ayyukan ci gaba.

Shugaban ya kuma soki tsarin yadda ake amfani da kudaden a yanzu, yana mai cewa gwamnonin Jihohi ke shirya zaɓen ƙananan hukumomi, inda ya ce tsarin ya fi kama da nada shugabanni sama da yin zaɓen dimokuraɗiyya na gaskiya da adalci.

Alegbere ya bayyana cewa ya na da fatan cewa gyaran kundin tsarin mulki da majalisar tarayya ke yi zai kawo karshen matsalar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: