Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi wa masu laifi 4,082 afuwa.

An yi wa masu laifin da ake kula da su a gidan ajiya da gyaran hali na ƙasar.
Ministan harkokin cikin gida Minta Olubunmi Tunji Ojo ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na shekara shekara da aka saba a Abuja.

A cewar ministan, afuwar da aka yi wa masu laifin zai taimaka wajen tseratar da naira miliyan dubu daya da ake kashewa kowacce.

Haka kuma gwamnatin ta amince da sauya matsugunin gidajen gyaran hali 29 bayan da su ka shigo cikin gari.
Daga cikin tsarin da su ka yi shi ne mayar da gidajen ajiya tazarar mita 100 daga cikin gari.