Tsohon gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekaru ya bayyana cewa babu hadakar da za ta iya hanbarar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027 mai zuwa.

Shekarau ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da Dr Sule Ya’u ya fitar, ya ce hadakar ‘yan adawar ba ta hada da shugabancin kowace jam’iyyar ba.

Shekarau na fadin hakan ne sa’o’i 48 kenan bayan da tsohon mataimakin shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ‘yan adawa sun shirya tsaf domin tunkarar shugaba Tinubu a zaben 2027, a wani taron manema labarai da suka yi a Abuja kan batun dunkulewarsu guri guda, da kuma sanya dokar tabaci da gwamnatin tarayya ta yi a Jihar Rivers kan rikicin siyasa.

Taron ya samu halarta tsohon gwaman Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufa’ da tsohon dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar Labour Party Peter Obi da dai sauransu.

Acewar Shekarau abu ne mai kyau hadewar wasu manyan ‘yan adawar, sai dai daga cikinsu babu wanda ya ke wakiltar jam’iyyarsa.

Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana cewa hadakar ‘yan adawar Kasar ba za a kira ta da hadin kan jam’iyyu ba, inda ya ce doka ce kadai za ta bayar da damar hadakar jam’iyyu ta hukuma.

Shekarau ya kara da cewa amincewa da Majalisar Tarayya ta yi da dokar tabaci da shugaba Tinubu ya ayya a Rivers ta nuna cewa ba su da wani iko da majalisar ko jam’iyyun adawa.

Ya ce ‘yan adawar da ba za su iya tabuka komai ba, sai dai idan sun haɗa da dukkanin shugabanni na jam’iyyun adawar Kasar a kowane mataki.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: