Sanata mai wakilatar Kogi ta Tsakiya a Majlisar attawa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta musanta rade-raden da ke yawo cewa ta nemi yafiyar Majalisar Dattawa bisa rikicin da ke faruwa tsakaninta da shugaban Majalisar.

Natasha ta musanta batun ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin, ta ce ba za ta taba neman afuwar Majalisar ba duba da cewa akan gaskiyarta ta ke.
Natasha ta kuma ce za ba ta sauka daga kan bakanta ba, inda ta ce rahotan bai’wa Majalisar hakuri da ake yadawa babu gaskiya a cikinsa kuma hakan na a matsayin yaudara.

Acewarsa an yi yunkurin sosai wajen ganin an rufe bakinta inda ta yi watsi da yunkurin, tana mai cewa za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka domin kare hakkin matan Najeriya har zuwa lokacin da aka fara sauraronsu.

Natasha ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jita da domin babu gaskiya a cikinsu, inda ta ce a halin yanzu ta tsaya ne akan gaskiya adalci, tare da kare mutanen da ta ke wakilta.
Idan ba a manta ba tun bayan wannan dambarwa da ta barke a tsakanin Sanata Natasha da shugaban Majalisar kan zargin lalata, kwamitin ladabtarwa na Majalisar ya dauki matakin dakatar da ita na tsawon watannin shiga sakamakon saɓawa dokokin majalisar.
