Wata tanka dakon mai ta kama da wuta a lokacin da ta ke sauke mai a gidan mai na A.A. Rano da ke garin Kontagora a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a misalin karfe 7:00 na dare jiya Lahadi, a kusa da babbaan Asibitin garin na Kontagora.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan tashin gobarar Tamkar man ce kawai ta Kone.

Tashin gobarar ta haifarwa da mutanen yankin tsoro sakamakon sauran tankunan man cike suke da man na fetur.
Rahotanni sun bayyana cewa ba a samu a sarar rayuka ba a yayin tashin gobarar.

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Husaini Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce bayan samun rahoton lamarin jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar sun isa gurin da wuri tare da dakile wutar don hanata yaduwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: