Ministan yada labarai Mohammed Idris ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai janye dokar tabaci da ya ayyana a Jihar Rivers ne bayan samun tabbatacce zaman lafiya a Jihar.

Ministan ya kuma ce shugaba Tinubu na da muradin ganin cewa Jihar ta Rivers ta koma cikakken mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda doka ta tanada.

Ministan ya bayyana haka ne a wata hira da Jaridar The Nation inda ya bayyana cewa komai yana daidaita a Jihar ta Rivers shugaban zai janye dokar da ya ayyana a Jihar.

Acewar Idris shugaban Tinubu ba shi da wata aniya ta karbe mulki ko nada gwamnan a Jihar ta Rivers kamar yadda wasu suke gani.

Muhammad ya ce daukar matakin ya zama dole ne bisa kundin tsarin mulkin Kasa, inda ya ce kundin tsarin mulki da harkokin mulki ya rushe baki daya a jihar ta Rivers, yayin da majalisar dokokin Jihar ta daina aiki yayin da bangaren zartarwa ke fuskantar matsaloli.

Ministan ya kuma ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi hakan, wanda hakan ya sanya Shugaba Tinubu ya dogara da dokar ƙasa wajen amfani da ikonsa domin ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: