Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya soke bikin hawan sallah da ya yi shirin yi a bana.

Ko da cewar sarkin bai ji daɗin matakin da ya ɗauka ba amma ya bayyana dalilan da ya sa ya soke bikin hawan.

A wani jawabi da sarkin ya yi ya ce ya soke bikin ne domin tsare rayuka, lafiya da dukiyoyin al’umma.

Ya ce ya ɗauki matakin hakan ne saboda kare dukan wata ƙofa ta fitina da ka iya fauwa sakamakon hawan da zai yi.

Sakin ya ce an yanke hukuncin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki ciki har da malamai da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce bikin hawan sallah da zai yi al’ada ce a don haka ba zai bari ta taɓa zaman lafiyar jihar Kano ba.

Sarkin a baya ya aike da wasiƙa ga jami’an tsaro don samar da su shirinsa na yin bikin hawan sallah a bana.

Hakan na zuwa ne kuma bayan da gwamnan jihar Kano ya umarci sarakuna da hakimai su fara shirin bikin sallah a bana.

Sanarwar umarnin bangarorin biyu ya haifar da rudani da kuma fargaba a zukatan al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: