Gwamnatin Kaduna Jihar ta amince da daukar ma’aikatan lafiya 1,800 a fadin Jihar.

Kwamishiniyar lafiya ta Jihar Hajiya Umma Ahmad ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis.
Sanarwar ta ce gwamnatin Jihar karkashin jagorancin gwamna Malam Uba Sani za a dauki Ma’aikatan ne domin cike gurbin Ma’aikatan a dukkan cibiyoyi kiwon lafiya matakin farko na Jihar.

Sanarwar ta kara da cewa daukar Ma’aiktan hakan zai kara tabbatar da ci gaban Jihar akan matsayin da ta ke dashi a fannin kiwon lafiya matakin farko a Najeriya.

Kwamishinyar ta kuma ce daukar ma’aikatar zai kawo karshen karancin ma’aikata da ake samu a cibiyoyin kiwon lafiyar, tare da raguwar yawaitar mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara, da kuma kara inganta lafiyar mutanen Jihar.
Acewarta a halin yanzu ana ci gaba da gyaran cibiyoyi 255 na kiwo lafiya matakin farko, yayin da za a daga martabarsu zuwa mataki na biyu, da samar da kayan aiki na zamani, tare da bayar da muhimman magunguna duk a kokarin da gwamnatin Jihar ke yi na inganta bangaren kiwon lafiya.
Kwamishinar ta kuma ce cibiyoyin za su dunga aikin duba masu cutuka daban-daban da suka hada da ciwon suga da bai yi karfi ba, hawan jini shima da bai yi karfi ba, da bayar da tallafin wajen haihuwa da dai sauransu.