Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu don yin bikin karamar sallah.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da ministan harkokin cikingida Tunji Ojo ya fitar jiya Laraba.

Sanarwar wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanyawa hannu,, an buƙaci al’umma da su yi amfani da lokaci wajen ɗabbaƙa zaman lafiya soyayya da ƙaunar juna.

Gwamnatin ta kuma buƙaci muslmi a Najeriya da su sanya ƙasar a addu’a don samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Haka kuma a sake sakata a addu’a don samun cigaba mai ɗorewa da kuma yin bukukuwan lami lafiya.

Ministan ya buƙaci al’ummar ƙasar musamman musulmi da su rungumi ɗabiar yafiya da ƙaunar juna tare da haɗin kai yadda za a gina Najeriya ta ci gaba da zama ƙasa ɗaya mai al’umma ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: