Gwamnonin jam’iyyar PDP a Najeriya sun shigar da ƙara a gaban kotun ƙoli don ƙalubalantar matakin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminilaye Fubara.

Gwamnonin Bauchi, Bayelsa da Adamawa, Osun Filato, da Enugu da Zamfara ne su ka shigar da ƙarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da majalisar dokoki ta ƙasa.

Gwamnonin sun ce matakin dakatar da gwamnan da aka yi ya saɓa da kundin tsarin mulkin ƙasar.

Gwamnonin na son babban kotun ƙolin ƙarƙashin babban mai sharia na ƙasa da su ayyana rashin iko ga shugaban ƙasa wajen dakatar da zaɓaɓɓen gwamna ƙarƙashin mulkin demokradiyya.

Haka kuma sun bukaci da a sanar da haramcin dakatar da majalisar dokoki da al’umma su ka zaba.

Gwamnonin dai sun ce shugaban ƙasa ba shi da iko na dakatar da gwamnan da aka zaba ko mataimaki da ma majalisar dokoki ta jiha.

A cewarsu hakan ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: