‘Yan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PRP a zaben 2023 na sun sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP.

Shugaban kungiyar ‘yan takarar gwamnan a PRP Malam Hayatuddeen Lawai Makarfi ya tabbatar da ficewarsu daga PRP zuwa SDP.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa sun dauki matakin koma SDP ne domin tsamo kasar nan daga halin da take ciki.

Lawai Makarfi wanda ya yi takarar gwamna a jam’iyyar ta PRP a Jihar Kaduna, ya bayyana cewa mutane na sauya sheka zuwa SDP ne bisa yadda da shugabancinta.

Makarfi ya ce sauya shekar su wani shiri ne na hadin domin kubtar da Najeriya daga shugabanci mara kyau, inda kuma ya nuna damauwarsa bisa yadda ake ci gaba da samun zubar jini, karuwar takauci, ya yin da hukumomin gwamnati ke durkushewa, inda kuma jam’iyyar APC da PDP suka mayar da mulkin kasar tamkar kasuwanci.

Kungiyar ‘yan takarar gwamnan ta kuma mika godiyarta ga PRP bisa damar da ta ba su a siyasa, inda suka ce a halin yanzu sun koma kan hanyar gaskiya.

Shugaban jam’iyyar SDP Malam Shehu Musa Gabam ya shaida musu cewa jam’iyyar za ta bai’wa masu sauya shekar dukkan wata dama da ta kamata.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: