Tsohon Mataimakin shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya musatan jita-jitar da ake yadawa ya karbi wasu kudade da aka ciro su daga Asusun gwamnatin Jihar Legas a zaben 2023 da ya gabata.

Atiku ya musanta batun ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Paul Ibe ya fitar a jiya Alhamis a Abuja, inda ya musanta zargin da ake yi masa na karbar kudaden daga hannun gwamnan Jihar Babajide Sonwo-Olu a zaben na 2023.

Sanarwar ta bayyana lamarin a matsayin wanda ba shi da inganci, don batawa Atikun suna a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Sanarwar ta bukaci mutane da su yi watsi da rade-raden, inda ta ce Atiku ya gudanar da yakin neman zabensa cikin gaskiya da amana, ba tare da yin wata alaka da kudin jihar ta Legas ba, kuma bai san gwamnan Jihar Sonwo-Olu ba, kuma ba su taba haduwa dashi.

Sananan Atiku ya kuma kalubalanci hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagin Kasa ta EFCC da ke binciken akan lamarin, inda ya bukace ta da ta fito ta bayyana sakamakon binciken da ta yi akai.

Atiku ya bayyana lamarin a matsayin wani makamin na siyasa, inda ya ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya daina amfani da siyasa wajen bata suna, inda ya ce hakan ba zai hana ‘yan adawa ci gaba da shirinsu na siyasa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: