Connect with us

Labarai

Za A Gudanar Da Addu’o’in Nema Wa Najeriya Tabbataccen Zaman Lafiya

Published

on

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa a yayin da shugaban Kasa Bola Tinubu ke cika shekaru 73 a duniya, zai a gudanar da addu’o’i na musamman a masallacin Kasa da ke Abuja a yau Juma’a.

Shugaba Tinubu zai cika shekaru 73 da haihuwa ne a gobe Asabar, 29 ga watan Maris 2025.

Mai magana da yawunsa kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis.

Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su gudanar da addu’a domin samun shiriya daga Allah, hadin kai da kuma yiwa kasar Addu’o’in samun tabbaccen zaman lafiya.

Sanarwar ta kara da cewa shugaba Tinubu zai sadaukar da ranar zagayowar ranar haihuwarsa ta hanyar komawa ga Allah da yin addu’o’in samun zaman lafiya, cigaba da kuma wadata a Najeriya.

Onanuga ya ce shugaba Tinubu zai yi amfani da lokacin a yau din wajen mika godiyarsa ga Allah bisa tsawaita rayuwarsa da ya yi, tare da ba shi damar shugabantar Najeriya.

Sanarwar ta ce shugaban ya yi amanna da cewa yin addu’in bai daya na da matukar muhimmanci wajen jagorantar kasar zuwa ga cigaba da kuma samun daidaito.

Sannan ya mika godiyarsa ga ‘yan Najeriya bisa goyon baya da kuma fatan alkhairi da ake yi masa, a lokacin da gwamnatinsa ke yin aiki tukuru don inganta tattalin arziki, karfafa tsaro, fadada samar da damarmaki ga ‘yan kasar, inda ya tabbatar da kudirinsa na karfafa dimokuradiyya, farfado da tattalin arziki, da kuma bunkasa hadin kan kasa.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar ‘Yan Arewa Da Aka Yiwa Kisan Killa A Jiharta

Published

on

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da gwamnan Jihar Edo Sanata Monday Okpehholo sun kai ziyarar ta’aziyya garin da mafiya yawa daga cikin mafarautan da aka kashe a Jihar Edo suka fito.

Gwamnan sun kai ziyarar ne a jiya Litinin, bayan gwamnan Jihar ta Edo ya zo Kano domin yin ta’aziyya ga gwamnan Kano da al’ummar Jihar kan kisan da aka yiwa Mafarautan.

A ziyarar gwamnan Abba, da gwamna Monday sun je garin Torankawa da ke Kano don yin ta’aziyyar mafarauta 16 da aka yiwa kisan Killa a Edo.

A yayin ziyarar gwamnan Gwamnan na Kano ya shaidawa ‘yan uwa da iyalan wadanda aka kashe cewa za a tabbatar da ganin an hukunta dukkan wadanda aka kama da hannun a cikin kisan.

Sannan gwamnan Abba ya ce gwamnatin Jihar ta Edo za ta yi kokarin ganin an biyasu diyyar ‘yan uwan na su.

Gwamna Abba ya kara da cewa za kuma a tabbatar da shaidawa duniya mutanen da suka yi aika-aikar tare da hukunta su don zama izina ga wasu.

Shima gwamnan na Edo ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da ganin an yi adalci a cikin lamarin, nan bada jimawa ba.

Continue Reading

Labarai

Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-wadai Da Kisan Da Aka Yiwa ‘Yan Yankin A Jihar Edo

Published

on

Kungiyar gwamonin Arewa ta yi tir da kisan mutane 16 da aka yiwa wasu mutanen yankin a Jihar Edo.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahya ne ya yi Allah-wadai da lamarin ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ibrahim Uba Misalli ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta ce bayyana cewa kisan mutanen ya sabawa doka da saba hakkin dan Adam, wanda ba za a lamunta da shi ba.

Gwamnan Yahya ya ce aika-aikar na barazana ga doka da oda, kuma kowane dan Najeriya na da ‘yancin tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ko wata barazana ba.

Kungiyar ta gwamonin ta ce ta damuwa matuka kan kisan mutane, inda ta ce ya zama wajibi a gano wadanda suka aikata kisan tare da kama su, da gurfanar da su gaban kotu cikin gaggawa, don hana sake faruwar hakan anan gaba.

Sanarwar ta gwamonin yankin na Arewa ta bakin shugabansu Muhammad Inuwa Yahya sun mika sakon jaje tare da ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu.

 

 

Continue Reading

Labarai

Wajibi Hukumomi Su Yi Komai A Bayyane Kan Kisan Gillar Da Aka Yiwa ‘Yan Arewa Edo

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai tare da nuna damuwar kan kisan gillar da aka yiwa wasu mafarauta a Jihar Edo.

Alhaji Atiku ya bayyana hakan ne ta cikin wata wallafa da ya fitar a yau Juma’a, yana mai bayyana cewa a yiwa dukkan wadanda aka kashe adalci.

Atiku ya bukaci hukumomin Kasar da su gagauta gudanar da cikakken bincike tare da yin komai a bayyana ne don daukar matakin doka akan wadanda suka yi aika-aikar.

Atiku ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe .

Continue Reading

Trending

%d bloggers like this: