Gwamnatin jihar Kano ta kare ƙudurin dokar yin ɓatanci da ta aiwatar dangane da hukuncin da kotun ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta yi, inda ta tabbatar da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata damar tsaftace ayyukan Addini a iya huruminta.

Hukuncin kotun ƙasashen yammacin Afirkan dai ya bayyana dokar ɓatancin a matsayin ba ta dace ba, ta kuma yi karo da gwadaben haƙƙoƙin ɗan’adam a duniya.

Sai dai cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kano Ibrahim Abdullahi Wayya ya fitar yau Lahadi, ya ce babu gudu ba ja da baya, don kuwa gwamnatin na da hurumin kiyaye tare da tabbatar da darajar al’ummar ta ta Musulmai waɗanda su ne mafi rinjaye.

Ya ce duk wata matsin lamba daga waje ba za ta sa guiwarsu ta yi sanyi ba, aikinsu ne ɗabbaƙa darajar al’ummarsu, wacce ta ke ta’allaƙe da addini da kuma kyawawan ɗabi’u, duk da cewa su na girmama dokokin ƙasashen duniya, amma ƙudurin al’ummarsu shi ne mafi a’ala.

Wayya ya ƙara cewa gwamnatin Kano na cikin tsarin tafiyar da mulkin tarayyar Najeriya, kuma an bai’wa jihohi ikon yin dokokin da za su kiyaye da kuma dace da yanayin zamantakewa, kyawawan ɗabi’u da kuma addinin al’ummominsu.

A ƙarshe ya bayyana cewa su na matuƙar girmama umarnin kotu, sai dai kuma dole ne dokokin jihar Kano su yi daidai da tsarin zamantakewa da addini al’ummarsu.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: