Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu, yayin da aka kuma samu asarar gonakin shinkafa da faɗinsu ya kai hekta dubu 10 bisa samun mummunar ambaliyar ruwa a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Mokwa, sakamakon sakin ruwa da hukumomi suka yi daga Madatsar Ruwa ta Jebba da ke jihar.
Shaidu gani da ido sun ce ambaliyar ta yi ɓarna mai yawa a gonakin yankin.

Shugaban Ƙungiyar Raya Yankin Kede Abdulraham Abdulƙadir Kede-Wuya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gonar shinkafarsa mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa.

Acewarsa gonakin da abin ya shafa dukkansu sun kai lokacin amfanin girbe su.
Shugaban ya ce an saki ruwan ne ba tare da sanar da mutane ba.
Shima wani manomi mai suna Ibrahim Ndako, ya bayyaana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa da wuya manoman su maida asarar da suka yi, ya mai kira ga hukumomi da su kawo musu dauki.
Mafiya yawa daga cikin manoman da suka yi noma a yankin sun fito ne daga jihohin Kano, Kebbi, Sokoto, Zamfara da kuma Borno, domin yin noman rani a yankin.