Mutane da dama ne suka fito zanga-zanga a Jihar Filato, bisa hare-haren ‘yan ta’adda da ake ci gaba da samu a wasu yankunan Jihar.

Masu zanga-zangar sun fito ne a yau Litinin a garin Jos babban birnin Jihar, inda mafiya yawa daga cikinsu kiristoci ne.
Masu zanga-zangar sun nuna damuwa da takaicin yadda ake ci gaba da kashe mutane a Jihar.

Shugaban kungiyar kiristoci ta Kasa CAN reshen Jihar Filato Rabaran Polycarp Lubo ne ya jagoranci zanga-zangar.

Shugaban ya ce sun gudanar da zanga-zangar ne domin ganin gwamnati ta dauki tsatstsauran mataki akan kashe mutanen da ake yi a Jihar.
Zanga-zangar na zuwa ne kwanaki kadan bayan haren-haren da ya yi sanadiyyar hallaka mutane sama da 100 a Jihar.