Wani hadarin mota da ya afku a Jihar Gombe yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane biyar, yayin da wasu Takwas suka jikkata a garin Billiri da ke Jihar.

Hadarin ya faru ne a yau Litinin a lokacin da mutanen ke tsaka da gudanar da bukukuwan Ester, inda wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi da ta tawo daga Jihar Adamawa ya afka kan taron mutanen da ke gudanar da bikin na Ester.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Buhari Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce bayan samun labarin faruwar lamarin, jami’an tsaro sun gaggauta kai ɗauki, inda suka ka kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Kakakin ya kara da cewa bayan faruwar lamarin wasu fusatattun matasa sun cinnawa motar wuta tare kuma da sace kayayyakin da ke cikinta.
Buhari ya ce jami’annasu sun samu nasarar wanzar da zaman lafiya a yankin.

Sannan ya ce kwamishinan ‘yan sandan Jihar Bello Yahya ya mika sakon jaje bisa faruwar lamarin ga ‘yan uwan wadanda abin ya shafa