Jam’iyyar PDP a Najeriya ta ce ficewar da aka samu na mambobinta a jihar Delta ya girgizasu matuka.

Sannan kuma cin amana ne na jam’iyyar haka kuma lamarin ya yi musu ciwo.
Shigaban jam’iyyar Umar Damagun ne ya ne ya bayyana haka a Abuja yayin mika takardar shaidar lashe zaben fidda gwani na gwamna Jude Ezenwafor na jihar Anambra.

A cewarsa Damagun, gangamin ficewa daga jam’iyyar da aka samu babban abin takaici ne a garesu.

A cewarsa, ba su taba tsammanin za a samu makamancin hak aa jihar Delta ba.
Sai dai ya nuna godiyarsa ga Allah kan cewar jam’iyyar ba ta yi musu komai ba.
Haka kuma ya ce jam’iyyar ta ga abinda ya fi haka amma kuma har yanzu ta na tsaye da kafafunta.
Gwamnan jihar Delta da mataimakinsa da kwamishinoninsa da ma waau da dama a jihar ne su ka fice daga jam’iyyar PDP su ka koma APC.
Haka kuma tsohon gwamnan jihar kuma tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP a shekarar 2023 shi ma ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.