Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ƙudurin gwamnatinsa na ɗaukar matakin gaggawa wajen dawo da aminci a dazukan da ‘yan ta’adda suka mamaye a Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar. Ya ce gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi sosai a bangaren fasaha da kayan leƙen asiri domin murkushe barayin daji, ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

Shugaban ƙasa ya bayyana haka ne a daren Juma’a yayin wata liyafar dare da aka shirya masa a gidan gwamnatin jihar Katsina, inda ya gana da dattawan jihar da shugabanni masu ruwa da tsaki.

Shugaba Tinubu ya ce, “Za mu yi amfani da dabaru na fasahar zamani domin mu kwato dazukan mu, za mu haɗa gwiwa da jihohi da kananan hukumomi don kare rayuka da dukiyoyi.”

Ya ce tsaro ba batun yanki ko jiha ba ne kaɗai, “Idan muna so a zuba hannun jari a Najeriya, tabbas sai mun daidaita sha’anin tsaro a ƙasar. Ba a zuba hannun jari a inda ake rikici.”

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa an fara ganin tasirin manufofin tattalin arzikin da ya aiwatar, musamman wajen farfaɗo da darajar naira da bunkasa kasuwanci.

Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta duba yiwuwar fadada filin jirgin saman Katsina domin samar da ayyukan yi da inganta sufuri.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya ce sun kafa rundunar tsaro ta musamman da ke tattara bayanan sirri domin taimakawa hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa an shirya fadada filin jirgin saman jihar da za a kashe Naira biliyan 54, wanda zai haifar da aikin yi kai tsaye ga mutum 2,700.

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yaba da jagorancin Shugaba Tinubu, ya kuma gode wa shugaban ƙasa bisa nadin ministoci biyu daga jihar da kuma dama da ya ba ‘yan asalin jihar da na Kaduna a hukumomin tarayya.

Liyafar ta samu halartar gwamnoni daga jihohin Kaduna, Jigawa, Borno, Benue, Yobe, Sokoto da Kwara, tare da sauran manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: