Gamayyar ƙungiyoyin ƴan asalin jihar Kano mazauna arewa maso gabashin Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril.

Gamayyar ƙungiyoyin ƙarƙashin jagiransu Dakta Adamu Ahmad sun jaddada kwarin gwiwarsu kan yadda Sanata Barau ke nuna kishi da kawo cigaba a jihar Kano.

A wata sanarwa da su ja fitar mai dauke da sa hannun Data Ahmad, sun ce hatta aikin kawo hukumar raya yankin arewa maso yamma babbar nasara wadda Sanata Barau ya jagoranci yi.

A cewarsu, sun cimma matsayar jaddada goyon bayansu a gareshi bayan bibiyar irin ayyukan da ya kawo jihar Kano, wanda ba za su lissafu cikin kankanin lokaci ba.

Daga cikin shirin da su ke yi akwai yunkurin tattara kan magoya baya yan asalin jihar Kano mazauna arewa maso gabas don nuna goyon bayansu.

Sanarwar ta ce wajibi ne su nuna goyon bayan saboda abinda ake bukata kenan na samun jajirtaccen wakili kuma jagora wanda dukkan cancantar da ake buƙata Sanata Barau na da ita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: