Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a yankin arewa maso yamma sun nuna goyon bayansu ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan zarcewarsa wa’adi na biyu a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

A wani taro da su ka yi q Kadunaz sun jaddada goyon bayansu ga shugaba Tinubu don sake zama shugaban ƙasa karo na biyu.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril a wajen taron sun ce babu gurbi a fadar shugaban ƙasa.

Ko da kae yadawa cewar ministan Abuja Nyesom Wike zai fito takarar shugaban ƙasa ya musnata tare da jaddada goyon bayansa ga shugaba Tinubu.

Taron ya samu halartar gwamnan Kaduna Malam Uba Sani, gwamnan Kebbi Nasir Idris, gwamnam jigawa Malam Umar Namadi.
Sannan akwai shugaban majalisar wakilai Tajudden Abbas, shugabannin jamiyyar a mataki daban-daban.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau ya jaddada kwarin gwiwarsu kaan cewar za su samu nasara a zaben da yake tafe.
Sanna ya bukaci da su ci gaba da hada kai da kuma aiki tare don samun nasarar.