Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Dr Suleiman Wali Sani mni, a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Jihar Kano.

 

Mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.

 

Sanarwar ta ce dawo da ofishin wani sashi ne na ƙoƙarin da gwamnatin Kano ke yi don ganin ta ƙarfafa shugabanci da sadar dashi ga al’ummar Jihar.

 

Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata gwamnatin Kano ta dakatar da Ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin bayan dakatar da Shehu Wada Sagagi daga kan kujerar, yayin da daga bisani kuma  aka naɗa shi a matsayin kwamishinan ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta Kano.

 

Dr Suleiman Sani ya kasance ƙwararren likita kuma masanin tsare-tsare, sannan ya kasance tsohon babban sakatare, inda ya kwashe sama da shekaru 40 yana aikin gwamnati cikin ƙwarewa.

 

Kafin naɗin Dr Sulaiman ya kasance mai bai’wa gwamna shawara na musamman kan harkokin ma’aikata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: